Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul bayt As ABNA ya habarta cewa: Hamas ta kara da cewa a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce sharuddan da aka ce Hamas ta fada na amincewa da yarjejeniya da Isra'ila kan musayar fursunoni da kuma tsagaita wuta a zirin Gaza ba su da tushe balle makama kuma cike da kage-kage.
Hamas ta kara da cewa: Wannan labarin karya ce karara wadda ba ta da alaka da matsayar kungiyar, kuma mun yi watsi da ita gaba daya.
Sanarwar ta Hamas ta bayyana cewa, manufar wadannan karairayi ita ce karkatar da ra'ayoyin jama'a daga laifukan yaki na gwamnatin sahyoniyawa ke aikatawa, da tunzura kungiyar Hamas da gwagwarmayar Palastinu, da kuma karkatar da matsayar kungiyar da ta bayyana.
Hamas ta jaddada cewa sharuddan kungiyar na duk wata yarjejeniya a fili suke kuma ana gabatar da su ne a bainar jama'a, ba ta hanyar wasu majiyoyi da ba a san sunansu ba wadanda ke yiwa gwamnatin mamayar Isra'ila hidima.
Hamas ta kara da cewa: A lokacin da gwamnatin sahyoniyawa ta kasa karya azama da iradar al'ummar Gaza, za ta kaddamar da kamfen din kafafen yada labarai na hadin gwiwa domin ruguza iradar al'ummar Gaza.
Your Comment